Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da karɓar mutane 21 da aka sace bayan nasarar wani aikin haɗin gwiwar jami’an tsaro, tare da kama mutane hudu da ake zargi da hannu a laifin satar mutane.
A cewar bayanan hukuma, an kubutar da mutanen ne a wani hari na bayanan sirri da aka kai a yankin tsaunukan Dargaza, a ƙaramar hukumar Danmusa.
Aikin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin haɗin gwiwar sojoji da 'yan sandan Najeriya da jami’an tsaron sa-kai na Al'umma.
Daga cikin waɗanda aka kubutar akwai mata 16 da maza biyu da jarirai uku.
Yawancin su an ce an sace su ne daga ƙauyen gidan sarkin Bayero da wasu yankunan da ke makwabtaka da ƙaramar hukumar Musawa.
Hukumomi sun bayyana cewa an kama mutanen hudu ne a yayin aikin, kuma suna ci gaba da bincike domin gano cikakkun bayanai da kuma cafke sauran da ke da hannu.
Gwamnatin jihar ta yaba da ƙwarewa da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, tana mai jaddada ƙudurin ta na ci gaba da yakar satar mutane da ‘yan bindiga domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
News Translation in English Language.
Security Forces Rescue 21 Abductees, Nab Four in Katsina Operation.
Katsina — Security agencies have rescued 21 abducted persons in Katsina State following a coordinated security operation that also led to the arrest of four suspects linked to kidnapping activities.
Officials said the victims were freed during an intelligence-driven raid conducted in the Dargaza Hills area of Danmusa Local Government Area.
The operation was spearheaded by the Department of State Services, working jointly with the Nigerian Army, the Nigeria Police Force, and local vigilante groups.
Those rescued included women, men, and infants, with security sources confirming that many were abducted from Gidan Sarkin Bayero village and surrounding communities in Musawa Local Government Area.
Authorities disclosed that four suspects were arrested at the scene and are currently in custody as investigations continue to dismantle the wider kidnapping network.
The state government praised the effective collaboration among security agencies and reiterated its resolve to sustain pressure on criminal elements in order to restore safety and stability across Katsina State.
Tags
Labarai
