Sojojin Fakistan sun gudanar da hare‑hare ta sama da jiragen marasa matuki a wasu sassan gabashin Afghanistan, musamman a yankin Paktika da Nangarhar, inda suka ce an kai farmaki kan sansanoni da mafakatan ‘yan ta’adda da ke da hannu a harin bam da aka kai a cikin Pakistan.
Hare‑haren sun biyo bayan jerin harin da aka kai ne a cikin Pakistan — ciki har da harin bam da ya kashe mutane a Islamabad da sauran hare‑hare a yankin arewa maso yammacin ƙasar — wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula.
Islamabad ta ce ‘yan ta’addan da ke hade da kungiyoyin Tehrik‑e‑Taliban Pakistan (TTP) suna shirin kai irin wadannan hare‑hare ne daga sansanoni da ke gefen Afghanistan.
Hukumomin Afghanistan sun yi martani mai zafi, suna cewa hare‑haren sun kashe fararen hula ciki har da mata da yara, har ma sun lalata makarantu da gidaje. Afghanistan ta bayyana cewa hare‑haren sun karya dokokin kasa da kasa kuma ta yi gargadin cewa za ta mayar da martani.
Pakistan ta bayyana cewa ‘yan ta’adda da ke Afghanistan na amfani da kasar a matsayin mafaka, kuma ta yi kira ga gwamnatin Taliban a Afghanistan da ta dauki mataki — wanda Afghanistan suka ki amincewa da shi, wanda hakan na daga cikin babban sabani tsakanin kasashen biyu.
Tags
Labarai
