PDP ta yi nasara kan APC a zaben ƙaramar hukumar Gwagwalada.


Jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaben shugaban Karamar Hukumar Gwagwalada na babban birnin Tarayyar Abuja (FCT). 
An bayyana Mohammed Kasim na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a jiya asabar, 21 Fabrairu 2026.

Sakamakon da aka fitar ya nuna cewa Kasim na Jam'iyyar PDP ya samu kuri’u 22,165, yayin da abokin hamayyarsa daga APC, Yahaya Shehu, ya samu kuri’u 17,788.

Kwamishinan Zabe na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Philip Akpeni , ya bayyana cewa zaben ya gudana cikin natsuwa da lumana kafin a sanar da Kasim a matsayin wanda ya yi nasara.

Wannan nasara ta PDP a Gwagwalada na nuni da rashin nasarar APC a wannan karamar hukumar, duk da cewa APC ce ke mulki a matakin tarayya. 
Zaben ya kasance wani bangare na zaben shekaran 2026 na babban birnin Tarayya Abuja, inda ake zaben shugabanni da ‘kansiloli a dukkan karamar hukumomi shida na Abuja.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form