Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa mai shekaru 40, James Milner, ya kafa sabon tarihi a gasar Premier League bayan ya zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan wasannin da aka taba bugawa a tarihin gasar.
Milner ya buga wasansa na 654 a gasar Premier League, inda ya zarce tsohon tarihi na wasanni 653 da Gareth Barry ke rike da shi. Wannan gagarumar nasara ta zo ne yayin da Milner ya buga wasa da Kungiyar sa ta Brighton & Hove Albion ta doke Brentford.
An san James Milner da jajircewa, ƙwarewa da tsawon lokacin da ya shafe yana taka leda a matakin kwararrun 'yan wasa, inda ya fara bugawa tun yana saurayi.
A tsawon wasannin shi, ya wakilci manyan kungiyoyi kamar Leeds United da Newcastle United da Aston Villa da Manchester City da Liverpool da Brighton.
Masana da masoya kwallon kafa sun yaba da wannan nasara, suna bayyana Milner a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan wasa a tarihin Premier League, kuma suna ganin wannan tarihi zai dauki dogon lokaci kafin wani ya iya karya shi.
News Translation in English Language.
James Milner Sets New Premier League Record for Most Appearances.
Veteran footballer James Milner, aged 40, has written his name into the history books after becoming the player with the most appearances in the Premier League.
Milner made his 654th Premier League appearance, surpassing the long-standing record of 653 games previously held by Gareth Barry. The milestone was achieved when Milner featured for Brighton & Hove Albion in their league match.
Known for his professionalism, versatility, and remarkable durability, Milner has enjoyed a career spanning more than two decades at the top level of English football. He has represented several clubs in the Premier League, including Leeds United, Newcastle United, Aston Villa, Manchester City, Liverpool, and Brighton.
Football analysts and fans alike have praised the achievement, describing Milner as a true Premier League legend whose appearance record may stand for many years to come.
