Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Bashir Ahmad Sani, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamnan Jihar Sokoto a zaɓen da ke tafe, lamarin da ya ja hankalin jama’a tare da haifar da muhawara a fagen siyasar jihar.
Malamin ya bayyana wannan mataki ne a wani taron manema labarai, inda ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne bisa kiran al’umma da kuma burinsa na kawo gyara a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a, musamman tsaro da ilimi da walwalar al’umma.
A cewarsa, kwarewarsa a harkokin addini da zamantakewa za su taimaka wajen samar da shugabanci na adalci da gaskiya da rikon amana.
Ya kuma jaddada cewa burinsa shi ne ya hada kan al’umma tare da inganta zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce shigar malamin addinin cikin takarar na iya sauya yanayin siyasa a Sokoto, duba da tasirin da shugabannin addini ke da shi a cikin al’umma.
Sai dai wasu na ganin za a fuskanci ƙalubale, musamman wajen raba addini da siyasa.
Ana sa ran wannan sanarwa za ta ƙara zafafa fafatawar siyasa a Jihar Sokoto yayin da ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban ke shirin fuskantar juna a zaɓen da ke tafe.
Tags
Labarai
_5.jpeg)