Hambararren Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolás Maduro, ya miƙa buƙata ga wata kotun tarayya a Amurka da ta watsar da tuhume-tuhumen laifi da ake masa, yana mai zargin cewa gwamnatin Amurka ta hana shi damar samun cikakkiyar kariya ta shari’a.
Lauyoyin Maduro sun bayyana cewa takunkumin da Amurka ta kakaba wa Venezuela ya hana a saki kuɗaɗen da ya kamata a yi amfani da su wajen biyan lauyoyin da zai zaɓa da kansa, lamarin da suka ce ya saba wa haƙƙin shari’a da kundin tsarin mulki ya tanada.
Sun ƙara da cewa, ko da yake wani lasisi ya fito na ɗan lokaci domin ba da damar biyan kuɗin kariya ta shari’a, an janye shi cikin gaggawa, abin da ya sake tsaurara matsalar. A cewarsu, wannan mataki ya tauye damar Maduro na samun adalci a gaban kotu.
Maduro na fuskantar tuhume-tuhume a Amurka da suka shafi fataucin miyagun ƙwayoyi da laifukan ta’addanci, zarge-zargen da ya musanta.
Ya ce matakan takunkumi da aka ɗauka a kansa ba wai kawai siyasa ba ne, har ma suna lalata tsarin adalci.
Masu sharhi na ganin wannan mataki na neman watsar da shari’a na iya ƙara ɗaga hankalin dangantakar diflomasiyya tsakanin Venezuela da Amurka, tare da janyo muhawara kan tasirin takunkumi ga haƙƙin ɗan Adam da shari’a.
News Translation in English Language.
Maduro Asks U.S. Court to Dismiss Criminal Charges.
Venezuela’s president, Nicolás Maduro, has filed a motion before a federal court in the United States, seeking the dismissal of criminal charges brought against him, alleging that the U.S. government has interfered with his right to a fair legal defence.
Maduro’s lawyers argue that U.S. sanctions imposed on Venezuela have prevented the release of funds needed to pay for legal representation of his choosing, a move they say violates his constitutional right to due process.
According to court filings, although a licence was briefly issued to allow the use of frozen funds to cover legal fees, it was withdrawn shortly after without explanation, further restricting Maduro’s access to legal counsel.
The Venezuelan leader is facing charges in the United States related to drug trafficking and narco-terrorism, allegations he has consistently denied. His legal team insists that the sanctions regime has gone beyond political pressure and now undermines the integrity of judicial proceedings.
Analysts say the motion to dismiss could further strain diplomatic relations between Venezuela and the United States, while also reigniting debate over the impact of economic sanctions on human rights and access to justice.
Tags
Labarai
