Shugaban Kanada Mark Carney Ya Ziyarci Indiya Domin Karfafa Huldar Kasuwanci.

Shugaban Kanada Mark Carney Ya Ziyarci Indiya Domin Karfafa Huldar Kasuwanci.

Shugaban Gwamnatin Kanada, Mark Carney, ya kai ziyara ta farko a Indiya domin karfafa hulda tsakanin kasashen biyu da bunkasa kasuwanci. 
Ziyarar na daga cikin kokarin Kanada na fadada dangantakar tattalin arziki da sauran kasashen duniya baya ga Amurka.

A yayin ziyarar, Carney zai gana da shugabannin kamfanoni da 'yan kasuwa domin tattaunawa kan yarjejeniyar kasuwanci da hadin gwiwa a fannonin makamashi da fasaha da ilimi da musayar al’adu, da kuma karfafa musayar albarkatun kasa kamar uranium.

Ziyarar na nuni da gyara a huldar Kanada da Indiya, bayan wasu matsaloli da suka faru a baya kan siyasa da al’ummar Sikh. 
Carney ya bayyana cewa manufarsa ita ce karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta hanyar kasuwanci ba tare da rikice-rikice na siyasa ba.

Haka zalika, wannan ziyara na daga cikin dabarun diplomasiya na Kanada na karfafa zumunci da kasashe masu tasowa kamar Indiya da Ostiraliya da Japan, domin bunkasa matsayi da tasirin Kanada a harkokin duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form