An Gano kaburburan Biyu Dauke da Gawarwaki Mutane 171 a Gabashin DR Kongo Bayan Ficewar ’Yan Tawayen M23.


Hukumomi da kungiyoyin fararen hula sun tabbatar da gano wasu kaburburan biyu dauke da gawarwaki akalla 171 a kusa da birnin Uvira da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano kaburburan ne a unguwannin Kiromoni da Kavimvira, inda aka ce kabari guda na dauke da gawarwaki kusan 30, yayin da dayan ke dauke da fiye da 140. 
Wannan ganowa ta biyo bayan ficewar kungiyar ’yan tawaye ta M23 daga yankin.

Shugabannin al’umma da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun zargi ’yan tawayen M23 da aikata kisan, suna cewa galibin wadanda aka kashe ana zargin su da goyon bayan sojojin gwamnati ko kuma kungiyoyin sa-kai masu mara wa gwamnati baya ne. 
Sai dai zuwa yanzu, kungiyar M23 ba ta amsa wannan zargi ba, kuma babu cikakken tabbatarwa daga masu bincike masu zaman kansu.

Masu lura da al’amura sun bayyana cewa rikicin da ke gudana a gabashin Kongo—wanda ke kunshe da kungiyoyin dauke da makamai sama da 100 da ke fafatawa kan yankunan da ke da albarkatun kasa—ya jawo mutuwar fararen hula da dama tare da tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu.

Rahoton, wanda kafar yada labarai ta Al Jazeera ta rawaito, ya nuna cewa ana ci gaba da bincike domin tantance adadin gawarwakin da kuma gano ainihin wadanda suka aikata wannan aika-aika.

News Translation in English Language.

Two Mass Graves with 171 Bodies Discovered in Eastern DR Congo After M23 Withdrawal.

Uvira, South Kivu — Authorities and civil society organisations have confirmed the discovery of two mass graves containing at least 171 bodies near the city of Uvira in eastern Democratic Republic of the Congo.

According to local officials, the graves were found in the Kiromoni and Kavimvira neighbourhoods. One of the sites reportedly contained around 30 bodies, while the second held more than 140. The discovery followed the recent withdrawal of the M23 rebel group from the area.

Community leaders and human rights groups have accused M23 fighters of carrying out the killings, alleging that many of the victims were suspected of having links to the Congolese army or pro-government militias. However, the M23 group has not responded to the allegations, and independent investigators are yet to confirm responsibility.

The discovery comes amid continued violence in eastern DR Congo, a region plagued by decades of conflict involving more than 100 armed groups competing for control of mineral-rich territories. The fighting has resulted in widespread civilian casualties and the displacement of millions of people.

The report, published by Al Jazeera, says investigations are ongoing to establish the full circumstances surrounding the killings and to identify those responsible.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form