Shehu Sani Ya Karyata El-Rufai kan Dadiyata, Inda ya ce ba Ganduje ya ke suka ba.

Shehu Sani Ya Karyata El-Rufai kan Dadiyata, Inda ya ce ba Ganduje ya ke suka ba.

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi watsi da ikirarin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi dangane da ɗan gwagwarmaya Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

A cewar El-Rufai, Dadiyata ba ya sukar gwamnatin Kaduna a lokacin mulkinsa, face ya karkata ne wajen sukar tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. 
Sai dai Shehu Sani ya bayyana wannan furuci a matsayin ƙoƙarin karkatar da gaskiya.

Shehu Sani ya ce bayanan da Dadiyata ya rika wallafawa a shafukan sada zumunta sun nuna a sarari cewa shi ɗan gwagwarmayar yana yin kakkausar suka ne kan manufofi da shugabancin gwamnatin Kaduna a lokacin El-Rufai, ba gwamnatin Kano ba.

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa Dadiyata ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu sukar salon mulkin gwamnatin Kaduna, lamarin da ya sa maganganunsa suka ja hankalin jama’a a faɗin ƙasar nan.

Batun Dadiyata dai na ci gaba da tayar da muhawara tun bayan ɓacewarsa a ranar 2 ga Agustan 2019, bayan da aka ce wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka sace shi daga gidansa da ke Kaduna. Har zuwa yanzu dai ba a samu bayani tabbatacce kan inda yake ba.

Rahotonni sun bayyana cewa muhawarar da ke tsakanin manyan ’yan siyasa kan rawar da Dadiyata ya taka na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya, musamman dangane da ’yancin faɗar albarkacin baki da kare haƙƙin ɗan Adam.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form