Majalisar Wakilai za ta gudanar da zaman musamman domin tattauna yiwuwar gudanar da zaɓen shekarar 2027 a cikin watan azumin Ramadan, abin da ke haifar da cece-kuce a sassan al’umma.
Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa zaɓen shugaban ƙasa zai gudana ne a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, wanda zai kasance a cikin ranakun azumi na Musulmai.
Sassan Musulmai da dama sun nuna damuwa, suna mai cewa gudanar da zaɓen a wannan lokaci zai iya kawo tangarda ga ibadar azumi.
Sai dai INEC ta bayyana cewa zaɓen ba a sanya ranakun ba ne kawai, har sai da aka bi dokoki da ka’idojin kundin tsarin mulki da na zaɓe, domin tabbatar da sahihanci da gaskiyar gudanar da zaɓe.
Tags
Labarai
