Shugabannin kasashe sama da 60, ministoci da jami’an tsaro daga kasashe fiye da 115 sun hallara a birnin Munich na ƙasar Jamus, domin halartar Taron Tsaro na Karo na 62 (MSC 2026).
Taron na shekara-shekara ne da aka kebe don tattaunawa kan manyan al’amuran tsaro da siyasar duniya.
A yayin zaman taron na kwanaki biyu, shugabannin zasu mai da hankali kan:
Hadin kai tsakanin Turai da Amurka, inda shugabannin Turai ke neman rage dogaro da Amurka a harkokin tsaro.
Tsare-tsaren tsaron Turai, ciki har da dabarun yaki da bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashe.
Yakin Rasha da Ukraine da barazanar tsaro a nahiyar Turai da ma duniya baki daya.
Taron na MSC ya kasance muhimmiyar dama ga shugabannin duniya wajen tattaunawa kan yadda za a samar da zaman lafiya, da kare muradun kasa da kasa daga barazanar duniya.
Masu sharhi sun bayyana cewa tattaunawar na nuna yadda duniya ke fuskantar manyan kalubale na siyasa da tsaro, inda ake bukatar hadin kai da dabarun gaggawa domin tabbatar da kwanciyar hankali.
Tags
Labarai
