Ɗan Kenya, Ezra Kering Ya Lashe Gasar tsere gudun Marathon ta Birnin Legas na 2026.

Ɗan Kenya, Ezra Kering Ya Lashe Gasar tsere gudun Marathon ta Birnin Legas na 2026.

Ɗan wasan tseren gudu na ƙasar Kenya, Ezra Kipchumba Kering, ya lashe gasar "Lagos City Marathon" ta shekarar 2026, bayan ya kammala tseren kilomita 42.195 cikin sa’o’i 2 da mintuna 11 da daƙiƙa 55.

Gasar, wadda ke jawo mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, ta gudana ne a safiyar yau Asabar a birnin Legas, inda ‘yan wasa masu ƙwarewa daga Afirka da sauran ƙasashe suka fafata. Nasarar Kering ta nuna ƙwarewa da jajircewarsa a fagen tseren marathon na duniya.

A bangaren mata kuwa, ‘yar ƙasar Habasha, Meseret Dinke ce, ta zo ta daya bayan ta kammala tseren cikin sa’o’i 2 da mintuna 37 da daƙiƙa 36, lamarin da ya ƙara jaddada rinjayen ‘yan gabashin Afirka a irin wannan gasa.

Daga cikin ‘yan Najeriya, Boyi Nyango shi ne ɗan ƙasar da ya fara ketare layin ƙarshe a rukunin maza, inda ya kammala cikin 2:25:32, yayin da Deborah Badung ta zama ‘yar Najeriya ta farko da ta kammala cikakken tseren a bangaren mata a cikin 2:55:46.

Masu shirya gasar sun bayyana cewa an tanadi kyaututtuka masu tsoka ga zakarun gasar, inda wanda ya zo na farko a rukunin maza da mata zai karɓi dala 50,000, yayin da aka tanadi lada ta musamman ga fitattun ‘yan Najeriya.

Gasar Marathon ta Birnin Legas na daga cikin manyan wasannin tseren gudu a Afirka, kuma tana ci gaba da ƙara ɗaukaka matsayin Legas a taswirar wasannin motsa jiki na duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form