Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, kuma Shugaban Majalisar Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya ayyana gobe Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, a matsayin ranar farko na watan azumin Ramadan.
Ya tabbatar da haka ne bayan ganin jaririn watan Ramadan a sassan Najeriya da dama a yammacin yau Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wanda ke daidai da ranar 29 ga watan Sha’aban a kalandar Musulunci.
Tags
Labarai
