Ayatollah Ali Khamenei ya ce "Iran ba za ta taba mika wuya ko amincewa da matsin lamba daga Amurka ba".

Ayatollah Ali Khamenei ya ce "Iran ba za ta taba mika wuya ko amincewa da matsin lamba daga Amurka ba".

Jagoran Addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya sake nanata tsauraran kalamai kan Amurka, duk da ci gaban tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da Amurka.

A cewar Khamenei, Iran ba za ta taba mika wuya ko amincewa da matsin lamba daga Amurka ba, inda ya bayyana cewa duk wani yunkuri na raunana kasar ba zai yi nasara ba. 
Wannan tsauraran kalaman na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawar nukiliya ta kaikaice a birnin Geneva, tare da shiga tsakani na Oman, domin sasanta rikicin shirin nukiliyar Iran da kuma yiwuwar sassauta takunkumin da aka kakaba mata.

Duk da kasancewar tattaunawa na gudana, Khamenei ya nuna rashin amincewa da niyyar Amurka, yana mai cewa Iran za ta ci gaba da kare 'yancinta da tsaron kasa. 
Hakanan ya gargadi cewa kasar a shirye take ta dauki mataki idan aka yi mata barazana.

Masu sharhi kan al’amuran diflomasiyya sun bayyana cewa Iran na tafiya ne a kan hanya biyu: tana ci gaba da tattaunawa domin cimma maslaha, sannan a lokaci guda tana amfani da tsauraran kalamai da nuna karfi domin kwantar da hankalin ‘yan kasa da kuma yin gargadi ga kasashen waje.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form