EFCC Ta Tsawaita Tsare Tsohon Gwamnan Kaduna, El-Rufai, Kan Binciken ₦432bn.

EFCC Ta Tsawaita Tsare Tsohon Gwamnan Kaduna, El-Rufai, Kan Binciken ₦432bn.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Tarayya, EFCC, ta tsawaita tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yayin da take ci gaba da bincike kan zargin almundahanar kudade har Naira biliyan 432.

Rahotanni sun bayyana cewa EFCC ta gayyaci El-Rufai zuwa ofishinta a Abuja domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi lamuni da kudaden da aka ce an sarrafa su ba bisa ka’ida ba a lokacin mulkinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Lauyan El-Rufai ya bayyana cewa tsohon gwamnan yana bayar da cikakken hadin kai ga jami’an tsaro, tare da neman a ba shi beli, yana mai jaddada cewa ba zai gudu daga bincike ba.

Ana sa ran EFCC na iya neman umarnin kotu domin tsawaita tsarewar sa, yayin da take kammala binciken. El-Rufai dai ya musanta duk wani laifi, yana mai cewa binciken yana da nasaba da siyasa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form