Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta sanar da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a yayin watan azumin Ramadan.
Daga Litinin zuwa Alhamis, ofisoshi za su fara aiki kamar yadda aka saba amma za su rufe da wuri a rana domin baiwa ma’aikata damar gudanar da ayyukan ibada da azumi.
A ranar Juma'a, ofisoshi za su rufe da wuri fiye da sauran ranakun domin baiwa ma’aikata lokaci kafin sallar Jumma’a da sauran ayyukan ibada.
Wannan mataki an dauke shi ne domin taimakawa ma’aikata Musulmi su daidaita aiki da ibada cikin sauki a lokacin wannan watan mai alfarma.
Haka zalika wasu jihohi a arewacin Najeriya kamar Jigawa da Kebbi suma duk sun yi irin wannan rage-lokaci na aiki ga ma’aikata a watan Ramadan.
Tags
Labarai
