Majalisar Dattawa Ta Rage Wa’adin Sanar da jadawalin zabe da Kwanaki 60 Saboda Azumin Ramadan.

Majalisar Dattawa Ta Rage Wa’adin Sanar da jadawalin zabe da Kwanaki 60 Saboda Azumin Ramadan.

Majalisar Dattawa Ta Rage Wa’adin Sanar da jadawalin zabe da Kwanaki 60 Saboda Azumin Ramadan.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da gyara a Dokar Zabe, inda ta rage wa’adi da Hukumar Zabe ta Kasa – INEC ke bukata wajen sanar da jadawalin babban zabe da kwanaki 60.

A karkashin sabon gyaran, wa’adin sanar da zabe ya ragu daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 300 kafin ranar gudanar da zabe. Majalisar ta dauki wannan mataki ne domin bai wa INEC damar samun sassauci wajen tsara jadawalin zaben 2027, musamman don kauce wa haduwa da watan Ramadan, wanda ka iya shafar halartar masu kada kuri’a da kuma shirye-shiryen zabe.

Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan majalisar sun bayyana damuwa cewa tsohon wa’adi na kwanaki 360 zai iya tilasta gudanar da zaben a lokacin Ramadan, lamarin ka iya janyo kalubale ga masu azumi da jami’an zabe.

Shugabannin majalisar sun ce gyaran dokar ba ya sauya tsarin kada kuri’a ko yadda ake kirga sakamako ba ne, sai dai yana mayar da hankali ne kan lokacin da INEC ke sanar da jadawalin zabe, domin tabbatar da adalci da saukin gudanarwa ga ‘yan kasa.

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da bibiyar sauye-sauyen da ake yi a Dokar Zabe, yayin da ake sa ran za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta sahihanci da karbar sakamakon zaben 2027.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form