Ƙasar Saudi Arabia ta sanar a hukumance cewa azumin watan Ramadan zai fara ne a gobe Laraba, bayan an tabbatar da ganin jinjirin watan a yammacin yau Talata.
Sanarwar ta fito ne daga hukumomin addini na ƙasar bayan kwamitin duban wata ya tabbatar da ganin jinjirin, abin da ke nuna ƙarshen watan Sha’aban da kuma shigowar watan Ramadan.
Da wannan sanarwa, al’ummar Musulmi a Saudiyya za su fara azumi daga safiyar Laraba, inda watan mai alfarma ke kunshe da ibada da azumi da sallah da karatun Alƙur’ani da ayyukan alheri.
Hukumomi sun bukaci al’umma da su yi amfani da wannan wata wajen ƙara kusanci da Allah, tare da kiyaye zaman lafiya da taimakon juna a tsakanin jama’a.
Tags
Labarai
