Cutar Lassa ta kashe mutum daya a jihar Kano, ya yin da wasu mutum biyu suka kamu da cutar.

Cutar Lassa ta kashe mutum daya a jihar Kano, ya yin da wasu mutum biyu suka kamu da cutar.

Hukumar Kula da Cututtuka ta jihar Kano (KNCDC) ta tabbatar da barkewar cutar Lassa a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa mutum daya ya mutu, yayin da wasu biyu suka kamu da cutar.

Wanda ya mutu, ma’aikacin Æ™asa da Æ™asa (MSF) daga Faransa ne, wanda ya fara jin rashin lafiya mako guda bayan isowarshi Najeriya.

Wadanda suka kamu da cutar sun hada da:

Likita daga Minjibir.

Mace da ta kasance ta kusa da wanda ya kamu da farko.

An riga an gano mutane 62 da suka yi hulÉ—a da waÉ—anda suka kamu a kananan hukumomi guda biyar, ciki har da 25 da ke cikin haÉ—ari sosai, inda 22 suka gwada lafiya, 3 suka tabbatar da cutar.

An fara bin sawun duk wanda ya yi hulÉ—a da wadanda suka kamu da cutar.
Matar da ta kamu tana karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, yayin da likitan ke a wurin keɓe marasa lafiya.

Hukumar lafiya ta yi gargadi ga jama’a kan tsafta da wayar da kan al’umma, da kuma magance berayen da ke yada cutar.

Cutar Lassa na yaduwa ne ta hanyar abinci ko kayan gida da beraye masu dauke da cutar suka taba, kuma tana iya yaduwa tsakanin mutane musamman a wuraren kiwon lafiya da babu kariya ta musamman.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form