Sama da masu zaɓe miliyan 1.5 ake sa ran zasu kada kuri'a a zaɓen Kananan Hukumomin babban birnin Tarayya Abuja.

Sama da masu zaɓe miliyan 1.5 ake sa ran zasu kada kuri'a a zaɓen Kananan Hukumomin babban birnin Tarayya Abuja.

Sama da masu rajistan zaɓe miliyan 1.5 a babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, ake sa ran za su kada ƙuri’a a zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026, bayan da dukkan jam’iyyun siyasa suka kammala yaƙin neman zaɓe.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta bayyana cewa akwai masu rajistan zaɓe 1,680,315, yayin da 1,587,025 suka karɓi katin zaɓe na dindindin (PVC)—wato kusan kashi 94.4% na masu rajistan.

Zaɓen zai gudana ne a kananan hukumomi shida na FCT: 
Abuja Municipal Area Council (AMAC), 
Bwari, 
Gwagwalada, 
Kuje, 
Abaji da 
Kwali. 
Gaba ɗaya, kujeru 68 ake fafatawa—shugabannin kananan hukumomi shida da ’yan majalisu 62.

A wani mataki na shirye-shirye, Ministan babban birnin Tarayyar, Nyesom Wike, ya ayyana ranar Jumma’a, 20 ga Fabrairu, a matsayin ranar hutu, tare da takaita zirga-zirga daga ƙarfe 8 na dare (Jumma’a) zuwa ƙarfe 6 na yamma (Asabar) domin sauƙaƙa wa masu jefa ƙuri’a.

INEC ta jaddada cewa zaɓe mai inganci kaɗai za a amince da shi wajen kada ƙuri’a, tare da gargadi kan sayar da ƙuri’a da sauran laifukan zaɓe. 
Haka kuma, an kammala shirye-shiryen na’urorin BVAS da jigilar kayan aiki, da tantance masu sa ido da ’yan jarida.

Jam’iyyun siyasa sun yi kira ga al’umma su fito su yi amfani da haƙƙinsu na zaɓe cikin lumana, yayin da wasu ’yan takara a wasu yankuna suka janye tare da mara wa wasu baya kafin ranar zaɓen.

News Translation in English Language.

Over 1.5 Million Voters Ready as FCT Area Council Elections Loom

More than 1.5 million registered voters in the Federal Capital Territory (FCT) are set to cast their ballots in the Area Council elections scheduled for Saturday, 21 February 2026, following the official conclusion of political campaigns.

The Independent National Electoral Commission (INEC) reported that out of 1,680,315 registered voters, 1,587,025 have collected their Permanent Voter Cards (PVCs), representing a 94.4% collection rate.

The elections will take place across the six FCT area councils: Abuja Municipal Area Council (AMAC), Bwari, Gwagwalada, Kuje, Abaji, and Kwali. A total of 68 seats are being contested — 6 chairmen and 62 councillors.

To facilitate voter participation, the FCT Minister, Nyesom Wike, declared Friday, 20 February, a public holiday, with a restriction of movement from 8 pm (Friday) to 6 pm (Saturday).

INEC emphasized that only valid PVCs will be accepted for voting and warned against vote buying and other electoral offences. Preparations, including BVAS device deployment, logistics, and accreditation of observers and journalists, have been completed.

Political parties have urged residents to exercise their voting rights peacefully and lawfully, with some candidates in select councils having withdrawn and endorsed rivals ahead of the polls.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form