Haɗarin mota ya yi sanadiyyar Mutuwar Mutane 18 a ƙasar Ƙasar.

Haɗarin mota ya yi sanadiyyar Mutuwar Mutane 18 a ƙasar Ƙasar.

Akalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu, yayin da uku suka jikkata, sakamakon wani haɗarin mota da ya auku a kan babban titin 30 June Axis , kudu da birnin Port Said na ƙasar Masar.

Rahotanni sun bayyana cewa motar ɗaukar kaya ce ta buge ƙaramar motar fasinja wacce ke dauke da ma’aikata zuwa gonakin kifi, inda hakan ya yi sanadiyyar mummunan haɗarin.

Hukumomin gaggawa sun kwashe wadanda suka ji rauni zuwa asibitoci don samun kulawa ta gaggawa. 
Gwamnan lardin ya fara bincike don gano musabbabin haɗarin, tare da tsara tallafi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Masar na fuskantar yawaitar haɗurran mota, musamman saboda gudu mai yawa da rashin ingantaccen yanayin hanyoyi, da rashin bin dokokin hanya yadda ya kamata, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dama a kowace shekara.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form