Babban jami’in da ke kula da ayyukan Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya, Rear Admiral Musa Bello Katagum, ya rasu a Masar bayan gajeriyar rashin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke ƙasar Masar, inda ya je domin karɓar kulawar lafiya. Mutuwarsa ta girgiza rundunar sojin ruwan Nijeriya da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya.
Wata sanarwa daga rundunar Sojin ruwan Najeriya ta tabbatar da rasuwarsa, inda ta bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen jami’i mai ƙwarewa da sadaukarwa wajen kare tsaron teku da martabar ƙasa.
Marigayi Musa Bello Katagum ya rike mukamin Babban Jami’in Ayyuka (Chief of Naval Operations), inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da aiwatar da manyan ayyukan tsaron ruwa a Nijeriya.
Kafin rasuwarsa, ya rike muƙamai daban-daban a rundunar, ciki har da sassan leƙen asiri da tsare-tsare na soja.
An bayyana cewa an yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.
Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya da manyan jami’an gwamnati sun miƙa ta’aziyya ga iyalansa da abokansa da dukkan ma’aikatan rundunar.
Rasuwar Rear Admiral Katagum ta bar babban gibi a fannin tsaron ruwa na ƙasar, musamman a wannan lokaci da ake ƙara ƙaimi wajen yaki da fashin teku da satar man fetur a tekunan Nijeriya.
News Translation in English Language.
Nigeria Mourns as Naval Operations Chief Rear Admiral Katagum Passes Away in Egypt.
Nigeria has been thrown into mourning following the death of Rear Admiral Musa Bello Katagum, the Chief of Operations of the Nigerian Navy, who passed away in Egypt after a brief illness.
According to official sources, the senior naval officer died in a hospital in Egypt, where he had travelled to receive medical treatment. His death was formally confirmed by the Nigerian Navy, which described him as a dedicated and highly professional officer whose service greatly strengthened the nation’s maritime security.
Rear Admiral Katagum served as Chief of Operations at the Naval Headquarters, where he was responsible for planning and coordinating major naval missions across the country’s waterways. Throughout his career, he held several strategic positions within the Navy, contributing significantly to operations against piracy, oil theft, and other maritime crimes.
The Navy noted that the late officer was widely respected for his discipline, leadership, and commitment to national service. He was buried in accordance with Islamic rites.
Condolences have continued to pour in from senior military officials, government representatives, and colleagues, who described his death as a major loss to Nigeria’s defence and security architecture. His passing comes at a critical time when the Navy is intensifying efforts to safeguard Nigeria’s territorial waters and maritime assets.
Tags
Labarai
