Gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da mutane 17 a gaban kotu bisa laifin yin fitsari da bayan-gida a wuraren jama’a, abin da ya sabawa dokokin tsaftar muhalli na jihar.
An gurfanar da mutanen a Kotun Majistare Bolade, inda kotun ta same su da laifi. Kotun ta yanke hukuncin tarar N40,000 kowanne, ko kuma zaman gidan yari na wata guda ga duk wanda bai iya biyan tarar ba.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewa yin fitsari da bayan-gida a fili laifi ne da ke barazana ga lafiyar jama’a.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da tsaurara matakan aiwatar da doka domin kare muhalli da lafiyar al’umma.
Wahab ya kuma yi kira ga mazauna Lagos da su rinka amfani da bayan-gidan jama’a da aka tanada, tare da bin ka’idojin tsaftar muhalli domin kiyaye lafiya da tsabtar birnin.
Tags
Labarai
