Pakistan ta ayyana yaki akan Kasar Afghanistan bayan ta yi ruwan wuta a babban birnin ƙasar Kabul.

Pakistan ta ayyana yaki akan Kasar Afghanistan bayan ta yi ruwan wuta a babban birnin ƙasar Kabul.

Birnin Kabul na Afghanistan ya girgiza sakamakon hare-haren bama-bamai da jiragen yakin Pakistan suka kai a safiyar yau, lamarin ya zo ne bayan Pakistan ta sanar da ayyana yaki a kan Afghanistan.

Rahotanni sun bayyana cewa an ji karar fashe-fashe masu karfi a sassa daban-daban na Kabul, yayin da ake ganin wutar kariya daga sama a sararin samaniyar birnin. Hukumomi a Pakistan sun ce hare-haren sun nufi cibiyoyin soja da sansanonin mayaka ne na Afghanistan.

Ministan tsaron Pakistan ya bayyana cewa hakurin kasarsa ya kare, yana zargin gwamnatin Taliban ta Afghanistan da goyon bayan hare-haren da ake kai wa sojojin Pakistan a kan iyaka. 
A cewarsa, hare-haren da aka kaddamar na da nufin kare tsaron kasa da kuma mayar da martani ga barazanar da ke karuwa.

A bangaren Afghanistan kuwa, jami’an Taliban sun yi Allah-wadai da harin, suna cewa Pakistan ta keta ikon kasa da dokokin kasa da kasa. 
Sun kuma yi barazanar daukar matakan ramuwar gayya idan hare-haren suka ci gaba.

Rikicin ya biyo bayan karuwar artabu a kan iyakar kasashen biyu a ‘yan kwanakin nan, inda bangarorin biyu ke musayar zargi kan hare-haren kan iyaka.

Masu sa ido na kasa da kasa na nuna fargabar cewa wannan sabon rikici na iya ta’azzara tsaron yankin, tare da yin kira ga bangarorin biyu da su rungumi tattaunawa domin kauce wa yaduwar yaki.

News Translation in English Language.

Kabul Hit by Bombings as Pakistan Declares ‘Open War’ on Afghanistan.

Explosions rocked Afghanistan’s capital, Kabul, early Friday after Pakistani warplanes reportedly carried out airstrikes, marking a sharp escalation as Pakistan officially declared what it described as an “open war” against Afghanistan.

Residents reported loud blasts and flashes in the sky across parts of Kabul, alongside sightings of anti-aircraft fire, indicating active aerial attacks. Pakistani authorities said the strikes targeted military positions and militant infrastructure, accusing Afghanistan’s ruling Taliban of allowing cross-border attacks against Pakistani forces.

Pakistan’s defence officials stated that the country’s “patience has run out”, arguing that repeated border assaults left Islamabad with no option but to respond militarily to protect its national security.

In response, Afghanistan’s Taliban-led administration condemned the airstrikes, calling them a violation of Afghan sovereignty and international law. Taliban officials warned that continued attacks could trigger retaliation.

The confrontation follows days of intense clashes along the disputed border between the two countries, with both sides trading accusations over artillery fire and armed incursions.

International observers have expressed concern that the situation could further destabilise the region, urging restraint and renewed diplomatic engagement to prevent a wider conflict.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form