An Gurfanar da Wani Dan Kenya kan Yaudarar Matasa Don shiga Yaƙin Rasha da Ukraine.

An Gurfanar da Wani Dan Kenya kan Yaudarar Matasa Don shiga Yaƙin Rasha da Ukraine.

Wani ɗan ƙasar Kenya mai suna Festus Omwamba ya gurfana a gaban kotu bisa zargin safarar mutane, bayan da ake tuhumarsa da yaudarar matasan Kenya da alkawarin aikin yi a ƙasashen waje, amma daga bisani aka tura su yin yaƙi tare da sojojin Rasha a yaƙin da take yi da Ukraine.

Hukumar masu gabatar da ƙara ta Kenya ta bayyana cewa Omwamba ya ruɗi akalla matasa 22, inda aka gaya musu cewa za su samu aikin yi mai tsoka a ƙasar waje. 
Sai dai bayan isarsu Rasha, wasu daga cikinsu sun tsinci kansu a fagen daga na yaƙin Rasha da Ukraine.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun samu nasarar ceto wasu daga cikin matasan a yankin Athi River kusa da Nairobi kafin tafiyarsu, yayin da wasu uku da suka riga suka isa ƙasar waje suka shiga yaƙi, kuma daga bisani suka dawo gida da raunuka.

Omwamba ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, yana mai roƙon kotu da ta wanke shi. Wannan lamari ya sake jaddada damuwar da ake ciki game da yaudarar ‘yan Afirka da ake yi don shiga yaƙin Ukraine, lamarin da ya sa iyalai da dama ke kira ga gwamnatoci da su ɗauki mataki domin dawo da ‘ya’yansu gida.

Masana tsaro na nuna cewa wannan shari’a na iya zama babban darasi ga hukumomi wajen ƙarfafa yaƙi da safarar mutane da kuma kare matasa daga faɗawa tarkon masu cin gajiyar rikice-rikicen duniya.

News Translation in English Language.

Kenyan Man Charged with Luring Youths to Fight for Russia in Ukraine War.

Nairobi, Kenya – A Kenyan national, Festus Omwamba, has been charged with human trafficking for allegedly deceiving young Kenyans with promises of overseas employment, only to send them to fight alongside the Russia military in the ongoing conflict in Ukraine.

Kenya’s Director of Public Prosecutions stated that Omwamba is accused of duping at least 22 young people, who were misled into believing they would receive high-paying jobs abroad. Once in Russia, some found themselves forced into frontline combat in the Ukraine war.

Security reports indicate that some of the youths were rescued in Athi River, near Nairobi, before they could depart, while three others who had already traveled were injured in combat and later returned home.

Omwamba has pleaded not guilty to the charges. The case highlights growing concerns over the recruitment of African nationals into the Ukraine war, prompting families to call on governments to take action to repatriate their loved ones.

Experts say the case serves as a cautionary tale for authorities to strengthen efforts against human trafficking and protect young people from being exploited in international conflicts.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form