INEC ta sauya ranar zaɓen shugaban Ƙasa na 2027 zuwa watan Janairu.

INEC ta sauya ranar zaɓen shugaban Ƙasa na 2027 zuwa watan Janairu.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta sanar da sauya jadawalin manyan zaɓukan shekarar 2027, inda ta matsar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar tarayya zuwa watan Janairu, tare da ɗage zaɓen gwamnan Jihar Osun.

A cewar sanarwar da INEC ta fitar a Abuja, zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar tarayya yanzu za a gudanar da su ne a ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2027, maimakon lokacin da aka saba gudanarwa a ƙarshen Fabrairu. 
Haka kuma, zaɓen gwamnoni da na Majalisun Jihohi an tsayar da su a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2027.

INEC ta bayyana cewa sauyin ya biyo bayan sabbin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 ne, wadda ta tilasta a sake daidaita jadawalin domin ya dace da ka’idojin doka.

Sabon Jadawalin Zaɓen:
Zaɓen Shugaban Ƙasa & Majalisar Ƙasa: 16 Janairu, 2027

Zaɓen Gwamnoni & Majalisun Jihohi: 6 Fabrairu, 2027

Fara Gangamin Yaƙin Neman Zaɓe: daga ƙarshen Agusta 2026 (gwargwadon matakin zaɓe)

Dole ne a dakatar da gangamin yaƙin neman zaɓe sa’o’i 24 kafin ranar kaɗa ƙuri’a, kamar yadda doka ta tanada.


Zaɓen Gwamnan Osun:
INEC ta kuma sanar da cewa zaɓen gwamnan Jihar Osun an sauya shi daga 8 ga watan Agusta, 2026 zuwa 15 ga Agusta, 2026, domin daidaita jadawalin da sabon tsarin doka.

Hukumar ta buƙaci jam’iyyun siyasa da ’yan takara da sauran masu ruwa da tsaki su bi sabon jadawalin yadda ya kamata, tana mai jaddada aniyar ta na gudanar da sahihin zaɓe cikin adalci da gaskiya a faɗin ƙasar Nigeria.

News Translation in English Language.

INEC Moves 2027 Presidential Election to January, Shifts Osun Governorship Poll

The Independent National Electoral Commission (INEC) has announced a revision of the 2027 election calendar, moving the presidential and National Assembly elections to January and rescheduling the Osun governorship election.

According to a statement released in Abuja, the Presidential and National Assembly elections will now take place on Saturday, January 16, 2027, instead of the previously scheduled late February dates. Meanwhile, governorship and state assembly elections are set for Saturday, February 6, 2027.

The commission stated that the changes follow provisions of the Electoral Act 2026, which required an adjustment of the electoral timeline to comply with the new legal framework.

Updated Key Dates:
Presidential & National Assembly elections: January 16, 2027

Governorship & State Assembly elections: February 6, 2027

Start of campaign period: From late August 2026, depending on the specific election stage

Campaigns must end 24 hours before each election day, in line with the law.


Osun Governorship Election:
INEC also announced that the Osun governorship election has been moved from August 8, 2026, to August 15, 2026 to align with the revised electoral timetable.

The commission urged political parties, candidates, and other stakeholders to strictly adhere to the new schedule, emphasizing its commitment to conducting free, fair, and credible elections across Nigeria.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form