Majalisar dokoki ta Peru ta kada kuri’ar tsige Shugaban Rikon Kwaryar ƙasar, José Jerí, bayan watanni hudu kacal da ya hau kujerar shugabancin ƙasar.
Majalisar ta kada kuri’u 99 yayin da 'yan majalisu 75 suka yi rinjaye akan 24 wajen amincewa da tsige Shugaban, (75–24), wanda suka zargeshi da aikata abubuwan da ba su dace ba, ciki har da ganawa da ‘yan kasuwa na China ba tare da bayyani ba da kuma sanya mata a mukamai na gwamnati da ake ganin akwai matsala a ciki.
Hukumar bincike ta fara gudanar da bincike kan yiwuwar cin hanci da rashawa da amfani da matsayi wajen samun riba daga waɗannan ganawar.
Jerí ya zama shugaban ƙasa a watan Oktoba 2025 bayan Majalisar ta tsige tsohuwar shugaban ƙasa, Dina Boluarte, saboda “rashin cancanta ta ɗabi’a.” Wannan ya zama wani bangare na tsarin da aka canja shugabanni bakwai a cikin kimanin shekaru goma.
Tsige shi ya zo ne kwanaki kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasar da aka tsara yi a ranar 12 ga Afrilu, 2026. Majalisar za ta zaɓi sabon shugaban rikon kwarya don jagorantar ƙasar har zuwa lokacin da sabon gwamnati za ta hau mulki.
Wannan lamari ya nuna rashin tabbas a harkokin siyasar Peru da kuma kalubalen da ƙasar ke fuskanta wajen gudanar da mulki cikin tsari da kwanciyar hankali.
Tags
Labarai
_1.jpeg)