A rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar, ta bayyana cewa ’yan kasuwar Arewa hudu ne ake zargin sun rasa rayukansu a yayin zanga-zangar lumana da ta karkata zuwa tashin hankali a wasu sassan birnin Port Harcourt na jihar Rivers, wadda aka ce an kai hari ga “yan Arewa.”
Shugabannin al’umma daga cikin Hausawa sun tabbatar da cewa waɗanda suka mutu daga cikin al’ummar su ne, inda ake ganin lamarin a matsayin mummunan rikici na kabilanci.
Rikicin ya samo asali ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Nchelem Samuel Festus a Igwuruta, lokacin da wata rigima ta barke tsakanin wani direban keke da ake zargin dan Arewa ne.
Bayan haka, an samu barkewar zanga-zanga a tituna daban-daban, inda wasu kayan ’yan kasuwar da aka danganta da Arewa suka lalace ko aka sace.
Shugabannin al’umma sun yi kira ga lumana, tare da gargadin kada a ɗauki dukan wani kabila a matsayin mai laifi, domin kaucewa karuwan rikicin.
Har zuwa yanzu, an tabbatar da cewa ’yan kasuwar Hausa hudu ne suka rasa rayukansu a rikicin.
Sai dai Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa ana gudanar da bincike domin sanin abun da ya haifar da mutuwar mutanen.
Masana harkokin tsaro da shugabannin al’umma sun yi gargadin cewa irin wannan rikici yana iya haifar da rikice-rikice mai girma idan aka dauki laifin mutum daya a matsayin na kabila baki daya, musamman a wuraren da ake samun bambancin kabilanci da addini.
Tags
Labarai
