Kotun Tarayya dake Abuja ta dage shari’ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, sakamakon rashin halartan zaman kotun a yau Laraba.
An tuhumci El-Rufai da sace bayanan sadarwa na gwamnatin tarayya da sauran laifuka da Hukumar DSS ta gabatar.
Shari’ar da aka shirya yi a yau 25 ga Fabrairu, 2026, ba ta ci gaba ba saboda El-Rufai bai samu daman baiyana gaban kotu ba.
Mai gabatar da kara, Oluwole Aladedoyin (SAN), ya shaida wa kotu cewa El-Rufai yana hannun ICPC, wanda hakan ya sa ba a samu damar kawo shi gaban kotu ba.
Hakimin kotu, Justice Joyce Abdulmalik, ta ce saboda rashin isarsa, neman belinsa ya zama mara ma’ana a wannan lokaci, don haka an dage shari’ar.
Hukumar DSS ta gabatar da karar laifuka uku da suka hada da sace sirrin waya na Mashawarci a harkokin Tsaro (NSA) ga shugaban ƙasar Najeriya, Mallam Nuhu Ribadu, wanda ake ganin ya saba dokokin tsaron yanar gizo na Najeriya.
El-Rufai da lauyoyinsa sun shigar da ƙara kan shari’ar, suna neman kalubalantar tuhumar bisa hujjojin doka da tsarin shari’a.
Haka kuma, tsohon gwamnan ya shigar da ƙarar kare hakkin ɗan adam kan ICPC kan binciken da aka kai gidan sa.
Shari’ar za ta ci gaba ranar 23 ga watan Afrilu, 2026.
News Translation in English Language.
Federal Court Postpones El-Rufai’s Arraignment to April 23.
A Federal High Court in Abuja has postponed the arraignment of former Kaduna State Governor Nasir El-Rufai to April 23, 2026, after he failed to appear in court on the scheduled date.
El-Rufai faces criminal charges filed by the Department of State Services (DSS), including unlawful interception of government communications and related offences. The arraignment, originally scheduled for February 25, 2026, could not proceed because he was not present in court.
Prosecution counsel, Oluwole Aladedoyin (SAN), told the court that El-Rufai was still in the custody of the Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC), making it impossible to produce him for arraignment. Justice Joyce Abdulmalik ruled that since El-Rufai was not physically before the court, any request for bail was premature, and therefore the case was adjourned.
The DSS filed a three-count charge accusing El-Rufai of illegally intercepting the phone communications of the National Security Adviser (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, in violation of Nigeria’s Cybercrime and Communications Acts.
El-Rufai’s legal team has also filed applications to challenge and quash the charges, citing constitutional and procedural grounds. Additionally, he has filed a fundamental rights enforcement suit against the ICPC, alleging an unlawful raid on his residence and seeking compensation.
The case is now scheduled to resume on April 23, 2026.
Tags
Labarai
_2.jpeg)