Anyi Jana'izar wasu 'yan kasuwa hudu daga ƙauyen Yandoya a Jos ta Arewa, wadanda suka gamu da ajalinsu Sakamakon harin 'yan ta'adda yayin da suke kan hanyar Jos zuwa Pankshin don kasuwancin takalma na mako-mako.
Rahotanni sun bayyana cewa, maharan da ba a tantance ba sun farmaki yan kasuwan, inda hudu suka rasa rayukansu, yayin da biyu suka tsira daga harin.
Anyi musu jana’iza a garin Kabristan Sabon Anguwa, a Barkin Ladi, domin kauce wa tashin hankali a Jos.
Shugabannin al’umma sun yi kira ga jama’a da su zauna lafiya tare da roƙon hukumomin tsaro da gwamnati su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da tsaro a jihar Filato ke fuskantar ƙalubale, inda wasu hare-hare a ƙauyukan Barkin Ladi da Riyom suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
News Translation in English Language.
Four Traders Killed in Ambush on Jos-Pankshin Highway, Buried in Barkin Ladi.
Four traders from the Yandoya community in Jos North LGA were killed by suspected armed assailants while traveling from Jos to Pankshin for their weekly shoe trading business.
Two others managed to escape the attack, but the four victims lost their lives. Their bodies were recovered and buried at Sabon Anguwa cemetery in Barkin Ladi, a measure taken to prevent tensions from escalating in Jos.
Community leaders urged residents to remain calm and called on security agencies and the government to step up efforts to protect lives and property.
The killings come amid ongoing security challenges in Plateau State, where recent attacks in rural communities of Barkin Ladi and Riyom LGAs have left multiple people dead, raising concerns over rising violence in the region.
Tags
Labarai
