Jagoran Juyin Juya Halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, na shirin gabatar da jawabi ga al’ummar ƙasar nan bada jimawa game da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan wurare masu muhimmanci a Iran, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati ya bayyana.
Rahotanni sun ce hare-haren sun ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka tare da Isra’ila, lamarin da ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin sabon yanayin fargaba.
Ana sa ran jawabin Khamenei zai fayyace matakin da Iran za ta ɗauka, da kuma saƙon da ƙasar ke son isarwa ga duniya dangane da hare-haren.
Majiyoyi sun nuna cewa jami’an tsaro da na siyasa na Iran sun shiga zaman gaggawa, yayin da al’ummar ƙasar ke jiran jawabin jagoran ƙasar domin sanin yadda gwamnati za ta mayar da martani.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan jawabi na iya zama mai muhimmanci wajen tantance ko rikicin zai ƙara faɗaɗa ko kuma a samu wata hanya ta rage zafinsa a yankin.
News Translation in English Language.
Khamenei to Address Nation Shortly After U.S. and Israeli Strikes on Iran.
Tehran, Iran — Iran’s Supreme Leader, Ayatollah Ali Khamenei, is expected to deliver a nationwide address within minutes following airstrikes carried out by the United States and Israel on key targets inside Iran, according to Iranian state television.
The strikes have sharply escalated tensions between Iran and its long-time adversaries, raising fears of a wider conflict across the Middle East. Iranian officials said the attacks hit strategic locations, prompting emergency security and political meetings in Tehran.
Khamenei’s address is widely anticipated to outline Iran’s official response and signal the direction of its next steps, as both regional and international observers closely monitor developments.
Political analysts say the speech could prove critical in determining whether the confrontation intensifies further or opens the door to diplomatic efforts aimed at de-escalation.
Tags
Labarai
