Harin Amurka da Isra’ila Kan Makaranta Babbar Laifi ne —inji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran.

Harin Amurka da Isra’ila Kan Makaranta Babbar Laifi ne —inji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya yi kakkausar suka kan abin da ya bayyana a matsayin harin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila da aka kai kan wata makaranta, inda ya ce lamarin babbar laifi ne karara da kuma tauye dokokin kasa da kasa.

Baqaei ya ce harin, wanda rahotanni suka nuna ya auku a kudancin kasar, ya janyo mutuwar dalibai da dama tare da jikkata wasu, lamarin da ya girgiza al’umma tare da tayar da hankulan jama’a a fadin kasar.

Ya kara da cewa kai hari kan fararen hula musamman yara da cibiyoyin ilimi sabawa ce da ka’idojin jin kai na kasa da kasa, yana mai kira ga kungiyoyin kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya da su dauki matakin gaggawa domin hukunta wadanda ke da hannu a harin.

Kakakin ya jaddada cewa Iran ba za ta yi shiru ba kan irin wadannan hare-hare, yana mai zargin United States da Israel da karya dokokin yaki da kuma haddasa rikici mai barazana ga zaman lafiyar yankin baki daya.

A cewarsa, irin wannan hari na nuna rashin mutunta rayukan bil’adama, tare da bukatar al’ummar duniya su nuna adawa a fili domin kare fararen hula daga hare-haren soji.

News Translation in English Language.

US-Israeli Attack on School a Grave Crime — Iran’s Foreign Ministry Spokesperson.

Iran’s Foreign Ministry spokesperson, Esmaeil Baqaei, strongly condemned what he described as a joint US-Israeli attack on a school, calling the incident a clear violation of international law and a serious crime.

Baqaei stated that the attack, reported to have occurred in the southern part of the country, resulted in the deaths of several students and injuries to others, shocking communities and alarming the public nationwide.

He added that targeting civilians, especially children and educational institutions, contravenes international humanitarian principles, urging international organizations and the United Nations to take immediate action to hold those responsible accountable.

The spokesperson emphasized that Iran will not remain silent in the face of such attacks, accusing the United States and Israel of violating the laws of warfare and fueling conflicts that threaten peace in the region.

According to Baqaei, this attack highlights a disregard for human life and underscores the urgent need for the global community to openly oppose such military assaults on civilians.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form