Kasashe Indonesia da Maroko, Kazakhstan da Kosovo da Albania sun yi alkawarin aika rundunonin sojoji domin shiga wani ƙungiyar soja ta duniya da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Gaza.
Wannan mataki na zuwa ne karkashin shirin (Kwamitin zaman lafiya), wanda shugaban Amurka, Donald Trump, ke jagoranta, domin tallafawa wajen sake gina yankin da horar da ‘yan sanda da inganta tsaro a Gaza.
Rundunar sojojin Indonesia za ta taka rawa a matsayin mataimakin kwamandan ƙungiyar, tare da yiwuwar aika dubban sojoji.
Shirin na "Kwamitin zaman lafiya" ya samu amincewar Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya (UNSC Resolution 2803), wanda ke bai wa ƙungiyar ikon gudanar da ayyukanta a Gaza.
Rundunar za ta fara aiki ne a kudancin Gaza, musamman a Rafah, inda za a gudanar da horo ga ‘yan sanda da kuma tallafawa gyare-gyaren gwamnati.
Haka zalika, ƙasashe kamar Masar da Jordan suna bayar da tallafi wajen horar da ‘yan sanda, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan wakilcin Palasɗinu da yadda rundunar za ta gudanar da ayyukanta cikin adalci da gaskiya.
Wannan ƙungiya ta ƙasa da ƙasa ba ta karkashin ikon rundunar Majalisar dinkin Duniya, sai dai amincewar Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta na tabbatar da halaccin aikinta.
Tags
Labarai
