Hukumar DSS Ta shirya gurfanar da El-Rufai a gaban kotun tarayya kan zargin Laifukan kutse a yanar gizo.

Hukumar DSS Ta shirya gurfanar da El-Rufai a gaban kotun tarayya kan zargin Laifukan kutse a yanar gizo.

Hukumar tsaro ta farar Hula ta Najeriya (DSS) ta bayyana cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 25 ga Fabrairu, 2026, bisa zargin aikata laifukan yanar gizo da kuma karya dokokin tsaron ƙasa.

A cewar DSS, ana zargin El-Rufai da shiga cikin ayyukan kutse da satar bayanan sadarwa ba tare da izini ba, lamarin da ake cewa ya sabawa Dokar Laifukan Yanar Gizo da Dokar Sadarwa ta Najeriya. Tuhumar ta ƙunshi laifuka guda uku da suka shafi tsaro da amfani da hanyoyin sadarwa ta haramtacciyar hanya.

Hukumar ta ce za ta gabatar da shaidun da suka dace a gaban kotu domin tabbatar da tuhumar da ake yi wa tsohon gwamnan.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form