Hukumomin Isra’ila sun kakabawa Falasɗinawa tsauraran matakai a kan zuwa Masallacin Al‑Aqsa domin sallar Juma’ar farko a watan Ramadan.
Rahotanni sun nuna cewa an amince wa mutane kusan 10,000 kacal daga Yammacin Kogin Jordan su shiga masallacin, inda aka sanya sharuddan izini na musamman da ƙa’idojin shekaru. Dubban masu ibada ne suka makale a wuraren binciken tsaro, wasu kuma aka hana su wucewa kwata-kwata.
Masu ibada sun bayyana damuwa kan yadda aka tsayar da su a mashigai daban-daban, ciki har da Qalandiya, lamarin da ya hana da dama gudanar da ibada a masallacin mai tsarki Kuma na uku a daraja ga Al'ummar musulmi.
Wannan Ƙuntatawar na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar ƙarin tashin hankali a yankin, musamman a lokacin watan Ramadan, inda Urushalima ta Gabas ke kasancewa cibiyar takaddama a rikicin Falasɗinu da Isra’ila.
Tags
Labarai
