Hukumar ‘‘Yan sandan Jihar Borno ta raba jimillar kudi naira ₦20,137,770.34 ga iyalan jami’an ‘yan sanda tara da suka rasu yayin aiki, a karkashin Shirin Inshorar Rayuwa na Rukunin (Group Life Insurance Scheme).
An gabatar da kudaden ne a wani bikin miƙa takardun ceki, domin tallafawa iyalan wajen ilimi da kiwon lafiya, da sauran bukatun yau da kullum.
Kwamishinan ‘‘Yan sandan Jihar Borno, CP Naziru Abdulmajid ne, ya jagoranci raba kudaden, yayin da DCP Ibrahim Sumaila ya isar da sakon daga Kayode Egbetokun wanda ya jaddada cewa kula da walwalar jami’an ‘yan sanda da iyalansu babban buri ne ga Hukumar.
Shirin Inshorar Rayuwa na Rukuni an kafa shi ne domin samar da tallafi da kwanciyar hankali ga iyalan jami’an da suka rasu a aiki. Wannan rabon kudade ya biyo bayan wani irin rabo da aka yi a watan Janairun 2026 inda aka bayar da kimanin naira miliyan 18.38 ga wasu iyalan jami’an da suka rasu.
Tags
Labarai
