Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun damke fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa bisa zarginta da wulakanta takardar Naira.
Dele Oyewale, mai magana da yawun hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ya tabbatar wa manema labarai kamun da aka yi mata a Abuja da yammacin yau Talata.
Ya bayyana cewa an kama jarumar ta Kannywood ne biyo bayan wani faifan bidiyo da ke nuna yadda ta ke share datti a hancinta ta hanyar amfani da takardar kudin Naira.
“Bayan fitowar faifan bidiyon, Hukumar ta dauki matakin ne ta hanyar gano ta tare da kama ta don amsa tambayoyi.
"A halin yanzu tana tsare a wurin da Hukumar ke tsare da ita yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike," in ji mai magana da yawun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ga manema labarai.
Oyewale ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Tags
Labarai
