A jiya ne babban kwamandan rundunar sojin Amurka mai kula da nahiyar Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson ya bayyana cewa, Amurka ta aike da wani karamin tawagar sojoji zuwa Najeriya.
Hakan na zuwa ne tun bayan harin da Amurka ta kai wa Kungiyar 'yan ta'addan daji a jihar Sokoto da Kwara a ranar Kirsimeti.
Babban Janar din ya ce an aike da tawagar Amurka ne bayan da kasashen biyu suka amince da cewa akwai bukatar a kara kaimi wajen yaki da barazanar ta'addanci a yammacin Afirka.
Tags
Labarai
