Hukumar shirya jarabawar makarantun sakandire ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta shekaran 2025 (SSCE).

Hukumar shirya jarabawar makarantun sakandire ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025

Hukumar shirya jarabawar makarantun sakandire ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta shekaran 2025 (SSCE).

Magatakardar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, wanda ya bayyana hakan a hedikwatar hukumar da ke Minna a jihar Neja, ya ce an yi jarabawar darussa goma sha shida, kuma mutane 96,979 ne suka yi rijistar jarrabawar.

Wannan adadi ya kunshi maza 51,823, wanda ke wakiltar kashi 53.43%, da mata 45,156, wanda ke wakiltar kashi 46.56%.

A cewarsa, Dalibai 68,166 da ke wakiltar kashi 71.63% cikin 100, sun samu nasara a darusa biyar da sama da haka, wadanda suka hada da Turanci da Lissafi.

Magatakardar ya kuma bayyana cewa mutane 82,082, wadanda ke wakiltar kashi 86.26% cikin dari, sun sami nasara a darusa biyar da sama da haka ba tare da la’akari da Harshen Turanci da Lissafi ba.

Ya bayyana cewa an yiwa ‘yan dalibai 9,016 katin shaidar cin jarabawa daban-daban, wanda hakan ya nuna an samu karuwar kashi 31.7 cikin 100 idan aka kwatanta da na 6,160 da aka samu a shekarar 2024.

Farfesa Wushishi yace an soke cibiyoyi hudu - biyu daga jihar Neja da daya daga jihohin Yobe da Kano - wadanda aka gano suna da hannu a taimakawa wajen satar jarabawa.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form