An kashe Saif al-Islam Gaddafi, dan tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi da ya dade a kasar Libya.

An kashe Saif al-Islam Gaddafi, dan tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi da ya dade a kasar Libya.

An kashe Saif al-Islam Gaddafi, dan tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi da ya dade a kasar Libya.

Wakilin Aljazeera a kasar Libya, Ahmed Khalifa, ya sanar da cewa, ana kyautata zaton wasu 'yan bindiga ne suka harbe Saif Gaddafi har lahira a birnin Zintan da ke yammacin kasar Libya, inda yake zaune tsawon shekaru goma da suka gabata.

Mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Abdullah Othman ne ya tabbatar da kisan nashi.

Saif al-Islam Gaddafi bai taba samun mukami a Libya ba, amma ana daukarsa a matsayin mai karfin fada aji a Libya baya ga mahaifinsa daga shekara a 2000 har zuwa shekaran 2011, lokacin da dakarun adawa na Libya suka kashe Muammar Gaddafi wanda ya kawo karshen mulkinsa na shekaru da dama.

An kama Saif al-Islam Gaddafi tare da daure shi a Zintan a shekara ta 2011 bayan yunkurin tserewa daga kasar bayan da 'yan adawa suka karbe birnin Tripoli.

Sai dai an sake shi a shekaran 2017 bayan an mashi afuwa.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: