Isra’ila na ci gaba tsaurara hare-hare da kwacen filayen Falasdinawa a yammacin Kogin Jordan.

Isra’ila na ci gaba tsaurara hare-hare da kwacen filayen Falasdinawa a yammacin Kogin Jordan.

Wani Rahoto da Kafar yada labarai na Al Jazeera ya fitar, ya bayyana cewa Isra’ila ta kara kaimi wajen kai hare-hare tare da kwace filaye a yankin Yamma da Kogin Jordan da ke karkashin mamayan Israi'la.

A cewar rahoton, sojojin Isra’ila tare da 'yan kama wuri zaunan yahudawa sun kara yawan samame a garuruwa da kauyukan Falasdinawa, inda ake rusa gidaje da lalata gonaki, da tilasta wa mazauna yankin barin muhallansu. Wasu iyalai sun ce an tilasta musu rushe gidajensu da kansu saboda barazana da tsangwama.

Rahoton ya kuma nuna cewa sabbin manufofin gwamnatin Israi'la na yin rijistar wasu filayen Falasdinawa a matsayin “mallakin gwamnati”, ya bai wa ‘yan Kama wuri zaunan yahudawa damar fadada zama a yankin. 
Lamarin da masana da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka bayyana a matsayin mataki na karbar yankin Falasdinawa ba tare da ayyana shi a hukumance ba.

Haka zalika a bangaren kasa da kasa, kasashe da dama na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah-wadai da matakin na Isra’ila, suna masu jaddada cewa irin wadannan ayyuka na karya dokokin kasa da kasa na kara dagula zaman lafiya a yankin.

Rahoton ya kara da cewa hare-haren ‘yan matsugunan sun jikkata Falasdinawa da dama tare da jawo asarar dukiya, lamarin da ke kara tsananta halin da fararen hula ke ciki a yankin Yamma da Kogin Jordan.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form