Wata coci a jihar Kaduna ta raba kayan abinci ga makarantun tsangaya da wasu Musulmai marasa galihu a matsayin tallafi na azumin watan Ramadan.
Shirin rabon kayan abincin ya samu jagorancin Church of Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Sabon Tasha, Kaduna.
An raba buhunan shinkafa da masara da sauran kayan abinci na yau da kullum domin rage wa jama’a radadin tsadar rayuwa a lokacin azumi.
Shugabannin cocin sun bayyana cewa wannan shiri na daga cikin kokarinsu na karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kiristoci a jihar, tare da tallafa wa mabukata musamman daliban makarantun tsangaya da iyalai marasa karfi.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun nuna godiya, suna cewa wannan taimako zai taimaka musu matuka wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.
Sun kuma bukaci sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni su rika taimakon marasa galihu, musamman a lokutan bukukuwa da azumi.
Tags
Labarai
_5.jpeg)