Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da rabon kayan tallafin azumin watan Ramadan ga gidaje 300,000 a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
Gwamnan ya ce shirin na da nufin rage radadin matsin tattalin arziki da talakawa ke fuskanta a lokacin azumin Ramadan, tare da tallafa wa iyalai masu karamin karfi.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da rabon kayan a birnin Maiduguri.
A cewar gwamnatin jihar, kowane gida da zai amfana zai karɓi:
* Buhun shinkafa guda ɗaya
* Buhun gero guda ɗaya
* Sukari kilo 10
Gwamna Zulum ya yi gargadi mai tsauri ga jami’an da ke da alhakin rabon kayan da su tabbatar da adalci da gaskiya, tare da hana duk wani yunƙurin karkatar da kayan ko sayar da su a kasuwa.
Ya kuma jaddada cewa ba Musulmi kaɗai ba ne za su amfana da shirin, inda ya ce Kiristoci da ke azumin Lent — wanda ya zo daidai da Ramadan a wannan shekara — su ma za a tallafa musu.
Gwamnan ya bukaci al’umma da su yi addu’o’i na zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki ɗaya, yana mai cewa irin wadannan shirye-shiryen tallafi na da muhimmanci wajen karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin jama’a.
_4.jpeg)