Iran ta ce a shirye take domin ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma ba zata lamunci kai mata hari ba.

Iran ta ce a shirye take domin ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma ba zata lamunci kai mata hari ba.

Iran ta ce a shirye take domin ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma ba zata lamunci kai mata hari ba.

Gwamnatin Iran ta bayyana cewa tana da niyyar komawa teburin tattaunawa da Amurka domin warware rikice-rikicen da ke tsakaninsu, musamman dangane da batun shirinta na nukiliya. 
Sai dai Iran ta jaddada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta idan aka kai mata hari ko aka yi mata barazanan soji ba.

Ministan harkokin wajen Iran ya ce duk wani hari, ko da kuwa karami ne, daga bangaren Amurka ko kawayenta, za a dauke shi a matsayin cin zarafi kai tsaye, kuma Iran za ta mayar da martani da ya dace. 
Ya kara da cewa kasar na fifita hanyoyin diplomasiyya, amma hakan ba zai hana ta daukar matakan kare ‘yancinta ba.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan Amurka ta nuna yiwuwar daukar matakan soji idan Iran ba ta amince da sharuddan da ake bukata ba. 
Rahotanni sun kuma nuna cewa Amurka na kara jibge dakarunta a yankin, lamarin da ke kara tayar da hankula.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa dawowar bangarorin biyu teburin tattaunawa na iya taimakawa wajen rage fargaba da kauce wa barkewar rikici mai fadi, duk da cewa har yanzu akwai rashin amincewa mai zurfi a tsakanin kasashen biyu.

Rahoton ya nuna cewa makomar tattaunawar za ta dogara ne kan yadda kowanne bangare zai nuna sassauci da kuma amincewa da hanyoyin sulhu maimakon karfin tuwo.

News Translation in English Language.

Iran Signals Openness to Dialogue but Warns It Will Respond to Any Hostile Action by the United States

Iran has reiterated its willingness to engage in diplomatic talks with the United States, stressing that dialogue remains its preferred path to resolving long-standing disputes, including issues related to its nuclear programme. At the same time, Tehran cautioned that it would respond firmly to any military aggression.

Speaking on behalf of the government, Iranian officials said that while diplomatic engagement offers a way to reduce tensions, Iran will not compromise on its sovereignty or national security. They warned that any attack—regardless of scale—would be viewed as a hostile act and met with a decisive response.

The remarks come as tensions continue to rise in the Middle East, with Washington maintaining that all options remain on the table should diplomatic efforts fail. Recent military movements in the region have further fuelled concerns about a potential escalation.

Analysts say the renewed signals of openness from Iran could provide an opportunity to de-escalate the standoff if matched by reciprocal steps from the United States. However, they note that years of mistrust mean any progress will require sustained commitment to diplomacy and confidence-building measures from both sides.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form