Aƙalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a sakamakon sabbin hare-hare da suka auku a wasu ƙauyuka da ke jihar Filato, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne a Barkin Ladi da Riyom, inda aka kai farmaki kan fararen hula ba gaira ba dalili.
Shaidun gani-da-ido sun ce wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa manoma ne da makiyaya, lamarin da ke nuna irin rikice-rikicen da suka daɗe suna addabar yankin.
Wasu mazauna yankin sun ce an kai harin ne da daddare, inda aka bude wuta kan mutanen da ke zaune lafiya, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
An kai waɗanda suka ji rauni asibitoci mafi kusa domin samun kulawar gaggawa.
Ƙungiyar Miyetti Allah shiyyar Nigeria ta nuna damuwa kan abin da ya faru, tana mai kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A nata bangaren, rundunar tsaro ta Operation Enduring Peace ta tabbatar da cewa ta fara bincike domin gano masu hannu a harin tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Gwamnati da shugabannin al’umma sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankula, su guji daukar doka a hannu, tare da haɗa kai da jami’an tsaro domin kawo ƙarshen tashin hankalin da ke faruwa a Jihar Filato.
News Translation in English Language.
Deadly Attacks in Plateau State Claim 12 Lives
At least 12 people have been killed following fresh attacks on communities in Plateau State, deepening security concerns in the region.
The attacks reportedly occurred in Barkin Ladi and Riyom local government areas, where armed assailants targeted unsuspecting residents. Eyewitness accounts indicate that both farmers and herders were among the victims, highlighting the persistent communal tensions in the area.
Residents said the assailants struck mostly at night, opening fire on civilians and causing multiple fatalities, while several others sustained injuries and were rushed to nearby hospitals for treatment.
The Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria expressed concern over the killings and urged the government and security agencies to take urgent steps to protect lives and property.
Meanwhile, the security task force Operation Enduring Peace confirmed that investigations have commenced to identify and apprehend those responsible, while efforts are being intensified to restore calm in the affected communities.
Authorities and community leaders have appealed for calm, urging residents to avoid reprisals and to cooperate with security agencies to prevent further violence in Plateau State.
Tags
Labarai
