Akalla mutane shida ne suka mutu, yayin da kimanin 46 suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin motar bas da ya afku a kan babbar hanyar BR-153 a jihar São Paulo dake kudu maso gabashin kasar Brazil.
Rahotanni daga hukumomin tsaro sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne bayan fashewar tayar mota, lamarin da ya sa direban bas din ya kasa ci gaba da sarrafa motar, inda ta kife a kan hanya.
An bayyana cewa mafi yawan fasinjojin da ke cikin bas din ma’aikatan gona ne, wadanda ke tafiya daga jihar Maranhão zuwa Santa Catarina domin aikin girbin ‘ya’yan itatuwa.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban domin samun kulawar gaggawa, sai dai har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan halin da lafiyarsu ke ciki ba.
Hukumomi sun ce an kaddamar da bincike domin gano hakikanin musabbabin hatsarin, tare da jaddada cewa hatsarurrukan manyan hanyoyi na ci gaba da zama babbar barazana ga rayuka a kasar Brazil, inda ake samun asarar rayuka masu yawa a kai a kai.
Tags
Labarai
