Hukumomin gasar Premier League na Ingila sun yanke shawarar dakatar da wasa na ɗan gajeren lokaci a watan Ramadan domin bai wa ‘yan wasa Musulmai da jami’an wasa damar yin buda baki (iftar) bayan faduwar rana.
Wannan dakatarwar ba za ta tsayar da wasan gaba ɗaya ba — za a yi ta ne a lokutan tsayawa na wasa, kamar throw-in, free-kick ko goal-kick, inda ‘yan wasan za su iya shan ruwa ko cin ɗan abinci cikin sauri.
An fara amfani da wannan tsarin ne a shekarar 2021, lokacin da aka dakatar da wasa tsakanin Kungiyar kwallon kafar Leicester City da Crystal Palace domin ‘yan wasa kamar Wesley Fofana da Cheikhou Kouyate su yi buda baki.
Kowane Kungiya da jami’an wasa suna yarda kafin wasan ko za a yi wannan dakatarwa, da kuma lokacin da ya kamata ayi, bisa la’akari da lokacin faduwar rana.
Dalilin wannan tsari shi ne girmama ibada da al’adar addini yayin da kuma ake tabbatar da wasan ya ci gaba ba tare da matsala ba. Wannan tsarin ya zama rabin al’ada a wasan Premier League idan Ramadan ya yi karo da kakar wasa, kuma ‘yan wasa da magoya baya sun amince da shi a matsayin mataki na haɗin kai da girmama addini.
