Gwamnatin Tarayya Ta bai wa wadanda Gobarar kasuwa ta shafa a jihar Kano tallafin naira biliyan 5.

Gwamnatin Tarayya Ta bai wa wadanda Gobarar kasuwa ta shafa a jihar Kano tallafin naira biliyan 5.

Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da Naira biliyan biyar (₦5bn) a matsayin tallafi ga ‘yan kasuwar da gobara ta rutsa da su a kasuwar Singer da ke Jihar Kano.

An bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai kasuwar, inda ya ce Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ne ya amince da tallafin domin taimaka wa ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyi sakamakon gobarar.

Shettima ya ce tallafin zai taimaka wajen farfado da harkokin kasuwanci da rage radadin da ‘yan kasuwar ke ciki, tare da jaddada cewa za a rarraba kudin cikin adalci da gaskiya ga wadanda abin ya shafa kai tsaye.

Gobarar ta lalata kayayyaki da kadarori masu yawa, lamarin da ya jefa daruruwan ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali. 
Hukumomi sun ce za su ci gaba da daukar matakan kariya domin hana aukuwar irin wannan bala’i a nan gaba.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form