Gwamnatin Mexiko Ta Tsaurara matakan Tsaro Bayan Kashe Shugaban masu safaran miyagun kwayoyi “El Mencho”.

Gwamnatin Mexiko Ta Tsaurara matakan Tsaro Bayan Kashe Shugaban masu safaran miyagun kwayoyi “El Mencho”.

Rundunar tsaro ta Mexiko ta kashe Nemesio “El Mencho” ne a wani aikin soji a Tapalpa dake jihar Jalisco. 
Wannan mataki na zuwa ne bayan tsauraran bayanai da shirin hadin gwiwa tsakanin rundunar Mexiko da hukumomin sirri na Amurka. 

El Mencho yana daya daga cikin mafiya karfi a harkar miyagun kwayoyi a Mexiko, kuma shugaba ne mai suna a duniya saboda harkokinsa na laifuka.

Bayan mutuwarsa, an samu tashin hankali a fadin kasar, inda kungiyoyin da ke da alaka da kartel din suka kona motoci, suka kafa shingen hanya, tare da kai hare-hare a jihohi da dama.
Rundunar soji ta tura dubban sojoji, kusan 10,000, musamman a jihar Jalisco, domin dawo da zaman lafiya. 
Haka kuma, an rufe makarantu da wasu hukumomi a birane da dama ciki har da Guadalajara, a matsayin matakin kariya.

Tashin hankalin ya shafi rayuwar yau da kullum, inda aka samu rufe makarantu da dakatar da ayyukan sufuri a wasu yankuna. Gwamnatoci ciki har da Amurka sun bayar da shawarwari ga matafiya da mazauna yankunan da abin ya shafa su tsaya a gida ko kaucewa zuwa wuraren da suka fi hadari.

Kashe El Mencho ya zama babban rashi ga Kungiyar ta CJNG, amma masana suna gargadin cewa rikicin iko a cikin Kungiyar zai iya janyo karin tashin hankali yayin da bangarori ke neman mulki a karkashin kungiyar.

News Translation in English Language.

Mexican Government Tightens Security After Killing of Drug Lord “El Mencho”.

The Mexican security forces have killed Nemesio “El Mencho” Oseguera Cervantes, leader of the Jalisco New Generation Cartel (CJNG), during a military operation in Tapalpa, Jalisco. The operation followed extensive intelligence gathering and collaboration between Mexican authorities and U.S. intelligence agencies.

El Mencho was one of Mexico’s most powerful drug traffickers and a globally notorious crime figure.

Following his death, widespread unrest erupted across the country, with cartel-linked groups setting vehicles and businesses on fire, establishing roadblocks, and carrying out attacks in several states. The military deployed thousands of troops, nearly 10,000, with a heavy presence in Jalisco to restore order. Schools and government offices in several cities, including Guadalajara, were closed as a precautionary measure.

The unrest disrupted daily life, with transportation halted and schools shut in affected areas. Governments, including the United States, issued advisories urging travelers and residents in impacted regions to remain indoors or avoid high-risk areas.

El Mencho’s death is a major blow to CJNG, but experts warn that internal power struggles within the cartel could lead to further violence as factions compete for control.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form