Hukumomi a jihar Legas sun Kama Mutane 46 Saboda yin bayan gida a waje.


Hukumar dake kula da tsafta ta Jihar Legas ta kama mutane 46 — maza da mata — saboda yin bayan gida a wurare marasa tsari a birnin Legas.

Rundunar Hukumar mai yaki da yin bayan gida a bainar Jama'a, ta gudanar da aikin ne da safe a wuraren da aka gano suna da matsalar rashin tsafta. 
Ayyukan sun gudana ne daga ranar 20 zuwa 22 ga Fabrairu, 2026, inda aka kama mutane a ranaku daban‑daban.

An fi mayar da hankali ne a yankunan Ebute Ero da Marina da CMS da Obalende da Adeniji Adele, inda ake yawan samun matsalar rashin tsafta.

Mutanen da aka kama za a tura su hedikwatar hukumar kula da muhalli da tsafta ta Jihar legas dake Oshodi don gudanar da bincike da kuma shari’a bisa dokokin muhalli na jihar.

Gwamnatin ta ce wannan matakin na daga cikin shirin yaki da bayan gida a waje, domin kare lafiya da tsaftar jama’a a fadin birnin.

Yin bayan gida a waje yana ɗaya daga cikin laifukan dokokin muhalli a jihar Legas, kuma yana kawo hatsarin lafiya saboda yaduwar cututtuka a wuraren da jama’a ke taruwa.

News Translation in English Language.

Lagos Cracks Down on Open Defecation, Arrests 46 Residents

Lagos, Nigeria — The Lagos State Government has arrested 46 residents for practicing open defecation across Lagos Island, authorities confirmed. The operation, led by the Anti-Open Defecation Squad, targeted known sanitation blackspots during early-morning enforcement drives between February 20 and 22, 2026.

The enforcement focused on densely populated areas including Ebute Ero, Marina, CMS, Obalende, and Adeniji Adele, where poor sanitation practices have persisted. Both men and women were apprehended during the sweep.

Those arrested have been taken to the Lagos State Environmental Sanitation Corps headquarters in Oshodi for investigation and prosecution under state environmental laws.

Officials described the crackdown as part of a broader initiative to eliminate open defecation, ensure public health, and uphold sanitation standards across the metropolis.

Open defecation remains a serious violation of environmental regulations in Lagos, posing significant public health risks, particularly in high-traffic commercial corridors.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form